15 Yuni 2025 - 04:51
Source: ABNA24
Mutane 23 Suka Mutu Tare Da Jikkata A Harin Makamai Mai Linzami Iran Ta Kai Kan Haifa

An kashe mutane 23 tare da jikkata a harin makami mai linzami da Iran ta kai kan Haifa

Harin makami mai linzami na IRGC a kan Haifa ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: majiyoyin yaren yahudanci sun buga wani rahoto kan hasarar rayuka da barnar da harin makami mai linzami na IRGC ya kai kan Haifa da kewayenta.

A cewar rahoton, harin makami mai linzami da Iran ta kai kan Haifa da kewaye ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku tare da jikkata wasu kimanin 20.

Ita ma matatar mai ta Haifa an kai harin makami mai linzami, kuma an ga wata babbar gobara ta tashi a Haifa.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun bukaci yahudawan sahyoniya da ke zaune a Haifa da kada su dauki hotunan wuraren da makamin ya fada a cikin birnin.

Your Comment

You are replying to: .
captcha